عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى رُخَصُهُ، كَمَا يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى عَزَائِمُهُ».
[صحيح] - [رواه ابن حبان] - [صحيح ابن حبان: 354]
المزيــد ...
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa".
[Ingantacce ne] - [Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi] - [صحيح ابن حبان - 354]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana son azo wa rangwaminSa wadanda ya shara'antasu, na sauki a cikin hukunce-hukunce da ibadu, da saukakawa a cikinsu ga wanda aka dorawa shari'a - kamar kasarun sallah da kuma hada su a halin tafiya -. Kamar yadda cewa Shi Yana son azo wa azimarSa, daga al'amura wajibai; domin umarnin Allah a rangwame da wajibai daya ne.