عَنْ حَكِيمِ بْنِ حِزَامٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَرَأَيْتَ أَشْيَاءَ كُنْتُ أَتَحَنَّثُ بِهَا فِي الجَاهِلِيَّةِ مِنْ صَدَقَةٍ أَوْ عَتَاقَةٍ، وَصِلَةِ رَحِمٍ، فَهَلْ فِيهَا مِنْ أَجْرٍ؟ فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَسْلَمْتَ عَلَى مَا سَلَفَ مِنْ خَيْرٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1436]
المزيــد ...
Daga Hakim Dan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce::
Na ce: Ya Manzon Allah, kana ganin abubuwan da nake ibada da su a lokacin Jahiliyya na sadaka ko 'yantawa, da sada zumunci, shin a akwai lada? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a agre shi - ya ce: "Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1436]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa idan kafiri ya musulunta to shi ana yi masa sakayya akan abinda ya kasance yana aikatawa a cikin Jahiliyya kafin musuluntarsa na ayyuka na gari kamar sadaka ne ko 'yanta bawa ko sada zumunci.