عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ اللهَ لَا يَظْلِمُ مُؤْمِنًا حَسَنَةً، يُعْطَى بِهَا فِي الدُّنْيَا وَيُجْزَى بِهَا فِي الْآخِرَةِ، وَأَمَّا الْكَافِرُ فَيُطْعَمُ بِحَسَنَاتِ مَا عَمِلَ بِهَا لِلَّهِ فِي الدُّنْيَا، حَتَّى إِذَا أَفْضَى إِلَى الْآخِرَةِ، لَمْ تَكُنْ لَهُ حَسَنَةٌ يُجْزَى بِهَا».

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana girman falalar Allah akan muminai, da kuma adalcinSa ga kafirai. Amma mumini ba za’a tauye ladan kyakkyawan da ya aikata ba; kai za'a ba shi ladan kyakkyawa anan duniya akan biyayyarsa, tare da abinda aka tanadar masa na sakayya a lahira; zai iya rabauta da kykkyawa gaba dayansa a lahira. Amma kafiri sai Allah Ya ba shi sakamakon abinda ya aikata na kyakkyawa da kyakkyawan duniya, har idan ya tafi lahira ba shi da wani ladan da za’a yi masa sakayya da shi a lahira; domin aiki na gari wanda zai yi anfani a duniya da lahira ba makawa mai shi sai ya zama mumini.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Lallai cewa wanda ya mutu akan kafirci ba wani aiki da zai yi masa anfana.
Kari