+ -

عَنْ خُرَيْمِ بْنِ فَاتِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الْأَعْمَالُ سِتَّةٌ، وَالنَّاسُ أَرْبَعَةٌ، فَمُوجِبَتَانِ، وَمِثْلٌ بِمِثْلٍ، وَحَسَنَةٌ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، وَحَسَنَةٌ بِسَبْعِ مِائَةٍ، فَأَمَّا الْمُوجِبَتَانِ: فَمَنْ مَاتَ لَا يُشْرِكُ بِاللهِ شَيْئًا دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ مَاتَ يُشْرِكُ بِاللهِ شَيْئًا دَخَلَ النَّارَ، وَأَمَّا مِثْلٌ بِمِثْلٍ: فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ حَتَّى يَشْعُرَهَا قَلْبُهُ، وَيَعْلَمَهَا اللهُ مِنْهُ كُتِبَتْ لَهُ حَسَنَةً، وَمَنْ عَمِلَ سَيِّئَةً، كُتِبَتْ عَلَيْهِ سَيِّئَةً، وَمَنْ عَمِلَ حَسَنَةً فَبِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، وَمَنْ أَنْفَقَ نَفَقَةً فِي سَبِيلِ اللهِ فَحَسَنَةٌ بِسَبْعِ مِائَةٍ، وَأَمَّا النَّاسُ، فَمُوَسَّعٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا مَقْتُورٌ عَلَيْهِ فِي الْآخِرَةِ، وَمَقْتُورٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا مُوَسَّعٌ عَلَيْهِ فِي الْآخِرَةِ، وَمَقْتُورٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمُوَسَّعٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ».

[حسن] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 18900]
المزيــد ...

Daga Khuraim Dan Fatik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ayyuka shida ne, mutane kuma hudu ne, akwai tabbatattu biyu. Da tamka da tamka, da kyakkyawa da tamkarta goma, da kyakkyawa da dari bakwai. Amma masu tabbatattu biyu: Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna. Wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta. Amma tamka da tamka: Wanda ya himmantu da kyakkyawa har ya jiyar da zuciyarsa ita, kuma Allah Ya santa daga gareshi za'a rubuta masa kyakkyawa, wanda ya aikata mummuna, za'a rubuta mummuna akansa. Wanda ya aikata kyakkyawa da tamkarta goma, wanda ya ciyar da wani abu a tafarkin Allah to kyakkyawa da dari bakwai. Amma mutane akwai wanda aka yalwatawa a duniya aka kuntata masa a lahira, da kuma wanda aka kuntatawa a duniya kuma aka yalwata masa a lahira, da wanda aka kuntatawa a duniya da lahira, da wanda aka yalwatawa a duniya da lahira".

[Hasan ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 18900]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ayyuka nau'uka shida ne, kuma mutane sinfi hudu ne. Ayyuka shidan su ne:
Na farko: Wanda ya mutu alhali shi ba ya tarayya da wani abu ga Allah to Aljanna ta tabbata a gare shi.
Na biyu: Wanda ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah wuta ta tabbata a gare shi yana madawwami a cikinta.
Su ne tabbatattu guda biyu.
Na uku: Kyakkyawa da aka niyyata, wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa kuma ya kasance mai gaskiya a cikin niyyarsa har sai ya jiyar da zuciyarsa hakan, kuma Allah Yana sanin wannan niyyar daga gare shi, sannan wani al'amari ya bijiro gareshi ba zai iya aikata wannan kyakkyawan ba za'a rubuta masa kyakkyawa cikakkiya.
Na hudu: Mummuna da aka aikata. wanda ya aikata wata mummuna za'a rubuta masa mummuna daya.
Su biyun: Tamka da tamka ne ba tare da ribanyawa ba.
Na biyar: Kyakkyawar da take da goma irinta, ita ce wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa ya kuma aikatata; za'a rubuta masa kyakkyawa goma.
Na shida: Kyakkyawar da take kasancewa da kaykkyawa dari bakwai, ita ce wanda ya ciyar da wata ciyarwa daya a tafarkin Allah sai a rubuta masa wannan kyakkyawar da kyakkyawa dari bakwai, wannan daga falalarSa ne - tsarki ya tabbara maSa Ya daukaka - da karamcinSa ga bayinSa.
Amma sinfin mutane hudu, su ne:
Na farko: Wanda aka yalwatawa a duniya daga arziki, aka ni'imtar da shi a cikinta yana samun abinda yake so a cikinta, saidai cewa shi abin kuntatawa ne a lahira kuma makomarsa ita ce wuta, shi ne kafiri mawadaci.
Na biyu: Wanda aka kuntatawa a duniya daga arziki, saidai cewa abin yalwatawa ne a lahira, kuma makomarsa ita ce Aljanna, wannan shi ne mmumini talaka.
Na uku: Wanda aka kuntatatawa a duniya da lahira, shi ne kafiri talaka.
Na hudu: Wanda aka yalwatawa a duniya da lahira, shi ne mumini mawadaci.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girman falalar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa da kuma ribanyawarSa ga kyawawan ayyuka.
  2. Adalcin Allah da karamcinSa, dan Ya mu'amalance mu a mummuna da adalci, sakamakon mummuna da daya ne.
  3. Girman shirka da Allah, domin a cikin shirka akwai haramta Aljanna ga wanda ya yi ta.
  4. Bayanin falalar ciyarwa a tafarkin Allah.
  5. Ribanya ladan ciyarwa a tafarkin Allah, yana farawa ne daga dari bakwai; domin hakan yana taimakawa akan daukaka kalmar Allah ne.
  6. Bayanin sinfofin mutane da kuma sabaninsu.
  7. Ana yalwatawa mumini a duniya da wanda ba mumini ba, amma ba a yalwatawa wani a lahira sai mumini kadai.