عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«يَأْتِي الشَّيْطَانُ أَحَدَكُمْ فَيَقُولُ: مَنْ خَلَقَ كَذَا؟ مَنْ خَلَقَ كَذَا؟ حَتَّى يَقُولَ: مَنْ خَلَقَ رَبَّكَ؟ فَإِذَا بَلَغَهُ فَلْيَسْتَعِذْ بِاللهِ وَلْيَنْتَهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3276]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3276]
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da maganin abinda ke taso da tambayoyin da Shaidan yake sa wasiwasi akan su ga mumini. Sai Shaidan ya ce: Waye ya halicci abu kaza? waye ya halicci kaza? waye ya halicci sama? kuma waye ya halicci kasa? Sai mumini ya ba shi amsa a Addinance da dabi'ance da hankalce da fadinsa: Allah ne. Saidai Shaidan ba ya tsayawa a wannan iyakar na wasiwasi, kai yana cirata har sai ya ce: Waye ya halicci Ubangijinka? A wannan yayin ne mumini zai ture wadannan wasiwasin da al'amaura uku:
Da yin imani da Allah.
Da neman tsarin Allah daga Shaidan.
Da kuma tsayawa kada ya zarce akan wasuwasin.