عن ابن عباس رضي الله عنهما قال:
جاءَ رجُلُ إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا رسولَ اللهِ، إن أحدنا يجدُ في نفسِهِ -يُعرِّضُ بالشَّيءِ- لأَن يكونَ حُمَمَةً أحَبُّ إليه من أن يتكلَّم بِهِ، فقال: «اللهُ أكبرُ، اللهُ أكبرُ، الحمدُ لله الذي ردَّ كيدَه إلى الوسوسَةِ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي في الكبرى]
المزيــد ...

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo gurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana ji aransa - ana bijiro masa da abu - ya zama toka shi ya fi masa da ya fadi maganar, sai ya ce: "Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya maida makircinsa zuwa wasiwasi".

Ingantacce ne - Abu Daud Ya Rawaito shi

Bayani

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana jin wani al'amari yana bijiro masa a zuciyarsa, saidai ya fade shi abu ne mai girma ne wanda ya kai matakin ace ya zama toka ya fi soyuwa agare shi akan ya fadeta. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kabbara sau biyu ya godewa Allah da ya mayar da kaidin Shaidan zuwa ga mujarradin wasuwasi.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin cewa Shaidan yana dakon muminai da wasuwasi; dan ya juyar da su daga imani zuwa kafirci.
  2. Bayanin raunin Shaidan game da ma'abota imani yayin da bai samu wani iko ba sai wasiwasi kawai.
  3. Yana kamata ga mumini ya bijirewa wasiwasin Shaidan da kuma tunkude shi.
  4. Halaccin kabbara yayin wani abu abin so ko mamaki, daga gareshi ko mai kama da shi daga al'amaura.
  5. Halaccin tambayar musulmi ga malami game da dukkanin abinda yake rikitar da shi.