+ -

عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: لَأُحَدِّثَنَّكُمْ حَدِيثًا سَمِعْتُهُ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ يُحَدِّثُكُمْ بِهِ أَحَدٌ غَيْرِي: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِنَّ مِنْ أَشْرَاطِ السَّاعَةِ أَنْ يُرْفَعَ العِلْمُ، وَيَكْثُرَ الجَهْلُ، وَيَكْثُرَ الزِّنَا، وَيَكْثُرَ شُرْبُ الخَمْرِ، وَيَقِلَّ الرِّجَالُ، وَيَكْثُرَ النِّسَاءُ حَتَّى يَكُونَ لِخَمْسِينَ امْرَأَةً القَيِّمُ الوَاحِدُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5231]
المزيــد ...

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wallahi zan zantar daku wani hadisin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanina ba zai zantar daku shi ba: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5231]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga alamomin kusantowar tashin Alkiyama dauke ilimi na shari'a, wannan kuwa ta hanyar mutuwar malamai ne. Sakamakon hakan jahilci zai yawaita ya yadu, zina da alfasha zasu yadu, shan giya zai yawaita, adadin maza zai karanta , adadin mata zai karu; har yakasance namiji daya zai tsayawa mata hamsin ga al'amuransu kuma zai jibinci maslahohinsu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin wasu daga cikin alamomin Alkiyama.
  2. Sanin lokacin Alkiyama yana daga al'amuran gaibu wadanda Allah ne kadai ya san su.
  3. Kwadaitarwa akan neman ilimin shari'a kafin a rasa shi..