عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى يَمُرَّ الرَّجُلُ بِقَبْرِ الرَّجُلِ فَيَقُولُ: يَا لَيْتَنِي مَكَانَهُ».

[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce wani kabari sai ya ce: Ina ma dai ni ne a wurin nan".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce kabari, sai ya yi burin ya zama matacce a bigirensa, sababi shi ne tsoronsa akan kansa na tafiyar Addininsa saboda rinjayar karya da ma'abotanta, da bayyanar fitintinu da sabo da abubuwan ki.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Nuni da bayyanar sabo da fitintinu a karshen zamani.
  2. Kwadaitarwa akan riko da kiyayewa da yi wa mutuwa tanadi ta hanyar yin imani da ayyuka na gari, da nisanta daga guraren fitintinu da bala'o'i.