+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى تُقَاتِلُوا اليَهُودَ، حَتَّى يَقُولَ الحَجَرُ وَرَاءَهُ اليَهُودِيُّ: يَا مُسْلِمُ، هَذَا يَهُودِيٌّ وَرَائِي فَاقْتُلْهُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2926]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai bayahude ya ce: Ya kai Musulmi, wannan bayahude ne ka kashe shi".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2926]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama ba zata tsayaba har sai musulmi da yahudawa sun yi yaki, Har idan bayahude ya gudu bayan dutse dan ya buyarwa musulmi; Allah zai sa dutsen ya yi magana ya kira musulmin: Da cewa akwai bayahude a bayansa har ya zo dan kashe shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bada labarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wasu daga abubuwan dake boye da masu zuwa, yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya tsinkayar da shi, to shi zai afku babu makawa.
  2. Yaki tsakanin musulmai da yahudawa a karshen zamani, kuma wannan yana daga alamomin Alkiyama.
  3. Wanzuwar addinin Musulunci har zuwa ranar Alkiyama, da nasararsa akan addinai gaba daya.
  4. Taimakon Allah ga musulmai akan makiyansu, daga wannan akwai sanya dutse ya yi magana a karshen zamani.