عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، لَيُوشِكَنَّ أَنْ يَنْزِلَ فِيكُمْ ابْنُ مَرْيَمَ حَكَمًا مُقْسِطًا، فَيَكْسِرَ الصَّلِيبَ، وَيَقْتُلَ الخِنْزِيرَ، وَيَضَعَ الجِزْيَةَ، وَيَفِيضَ المَالُ حَتَّى لاَ يَقْبَلَهُ أَحَدٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2222]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2222]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa akan kusancin saukar (Annabi) Isa dan Nana Maryam - aminci ya tabbata agare shi - dan ya yi hukunci a tsakanin mutane da adalci da shari'ar Annabi muhammadu, kuma shi zai karya gicciyayye (kros) wanda kiristoci suke girmama shi, kuma Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai kashe alade, kuma cewa shi aminci ya tabbata agare shi zai sarayar da jiziya zai dora mutane gaba dayansu a shiga Addinin Musulunci. Kuma dukiya za ta yawaita wani ba zai karbeta ba; dan yawanta, da wadatuwar kowa da abinda ke hannunsa, da saukar albarka da malalowar alkairai.