+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا، فَإِذَا طَلَعَتْ فَرَآهَا النَّاسُ آمَنُوا أَجْمَعُونَ، فَذَلِكَ حِينَ: {لاَ يَنْفَعُ نَفْسًا إِيمَانُهَا لَمْ تَكُنْ آمَنَتْ مِنْ قَبْلُ، أَوْ كَسَبَتْ فِي إِيمَانِهَا خَيْرًا} [الأنعام: 158] وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدْ نَشَرَ الرَّجُلاَنِ ثَوْبَهُمَا بَيْنَهُمَا فَلاَ يَتَبَايَعَانِهِ، وَلاَ يَطْوِيَانِهِ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدِ انْصَرَفَ الرَّجُلُ بِلَبَنِ لِقْحَتِهِ فَلاَ يَطْعَمُهُ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَهُوَ يَلِيطُ حَوْضَهُ فَلاَ يَسْقِي فِيهِ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدْ رَفَعَ أَحَدُكُمْ أُكْلَتَهُ إِلَى فِيهِ فَلاَ يَطْعَمُهَا».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6506]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu, wannan yayin da: {Wani rai imanin sa ba zai anfane shi ba, bai yi imani ba kafin nan, ko bai aikata alheri a imanin na sa ba} [Al-An'am: 158] kuma lalli Alkiyama za ta tsaya alhali mutum biyu za su shinfida tufafinsu a tsakaninsu ba za su saida shi ba, ba kuma za su ninkeshi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali hakika mutum ya juya da nonon taguwarsa da ta tatsa ba zai dandane shi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali shi yana yabe tafkinsa ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tsaya alhali hakika dayanku ya daga lomarsa zuwa bakinsa ba zai cinyeta ba".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6506]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa daga alamomin Alkiyama manya; shi ne bullowar rana daga yamma maimakon daga gabas, lokacin da mutane suka ganta za su yi imani gaba daya, A wannan lokacin imanin kafiri ba zai anfanar da shi ba, kuma aiki na gari ba zai yi amfani ba haka kuma tuba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama zata zo kwatsam; har cewa ita zata tashi alhali mutane suna cikin harkokin su da kuma sha'aninninkan rayuwarsu; Sai Alkiyama ta tashi alhali mai siyarwa da mai saya sun shimfida tufafinsu a tsakakninsu, amma ba za su saida su ba, ba kuma za su ninke su ba. Kuma Alkiyama zata tashi alhali hakika mutum ya dauki nonon taguwarsa mai yawan nono amma ba zai sha shi ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum yana gyara tafkinsa yana tsaftace shi amma ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum ya daga lomarsa zuwa bakinsa dan ya ci amma ba zai ci ba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Musulunci da tuba ana karbar su matukar rana ba ta bullo ta mafadarta ba.
  2. Kwadaitarwa akan tanadi dan Alkiyama da aiki na gari; domin Alkiyama za ta zo ne kwatsam..