+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى يَتَقَارَبَ الزَّمَانُ، فَتَكُونَ السَّنَةُ كَالشَّهْرِ، وَيَكُونَ الشَّهْرُ كَالْجُمُعَةِ، وَتَكُونَ الْجُمُعَةُ كَالْيَوْمِ، وَيَكُونَ الْيَوْمُ كَالسَّاعَةِ، وَتَكُونَ السَّاعَةُ كَاحْتِرَاقِ السَّعَفَةِ الْخُوصَةُ».

[صحيح] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 10943]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna, sai shekara ta zama kamar wata, wata kuma ya zama kamar Juma'a (sati guda), Juma'a kuma ta zama kamar yini, yini ya zama kamar awa, awa kuma ta zama kamar konewar ganyen dabino".

[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 10943]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa daga alamomin Alkiyama akwai kusantowar zamani, sai shekara ta wuce kamar yadda wata yake wucewa, wata kuma ya wuce kamar yadda sati yake wucewa, Juma'a (sati) ya wuce kamar yadda yini yake wucewa, yini ya wuce kamar yadda awa daya take wucewa, awa ta wuce da gaggawa mai tsanani kamar yadda ganyan bishiyar dabino yake konewa.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Daga alamomin Alkiyama cire albarka a zamani ko gaggawarsa.