عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ العَاصِ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ اللهَ سَيُخَلِّصُ رَجُلًا مِنْ أُمَّتِي عَلَى رُءُوسِ الْخَلَائِقِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، فَيَنْشُرُ عَلَيْهِ تِسْعَةً وَتِسْعِينَ سِجِلًّا، كُلُّ سِجِلٍّ مِثْلُ مَدِّ الْبَصَرِ، ثُمَّ يَقُولُ: أَتُنْكِرُ مِنْ هَذَا شَيْئًا؟ أَظَلَمَكَ كَتَبَتِي الْحَافِظُونَ؟ فَيَقُولُ: لَا يَا رَبِّ، فَيَقُولُ: أَفَلَكَ عُذْرٌ؟ فَيَقُولُ: لَا يَا رَبِّ، فَيَقُولُ: بَلَى إِنَّ لَكَ عِنْدَنَا حَسَنَةً، فَإِنَّهُ لَا ظُلْمَ عَلَيْكَ الْيَوْمَ، فَتُخْرَجُ بِطَاقَةٌ فِيهَا: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، فَيَقُولُ: احْضُرْ وَزْنَكَ، فَيَقُولُ: يَا رَبِّ مَا هَذِهِ الْبِطَاقَةُ مَعَ هَذِهِ السِّجِلَّاتِ؟ فَقَالَ: إِنَّكَ لَا تُظْلَمُ، قَالَ: فَتُوضَعُ السِّجِلَّاتُ فِي كِفَّةٍ، وَالْبِطَاقَةُ فِي كِفَّةٍ، فَطَاشَتِ السِّجِلَّاتُ، وَثَقُلَتِ الْبِطَاقَةُ، فَلَا يَثْقُلُ مَعَ اسْمِ اللهِ شَيْءٌ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 2639]
المزيــد ...
Daga Abdullahi dan Amr dan Al-Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 2639]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Zai zabi wani mutum daga al'ummarsa agaban halittu , za'a kira shi dan a yi masa hisabi, sai (Ubangiji) ya bijiro masa da fayilillika casa'in da tara, su ne takardun ayyukansa wadanda ya kasance yana aikatasu a duniya, kuma tsawon kowane fayil tamkar iya ganinnka ne. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: Shin kana musun wani abu daga abinda aka rubuta a cikin wadanannan fayilillikan? Shin Mala'ikuna masu kiyayewa masu rubutu sun zalinceka?. Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Shin kana da wani hanzari da za'a yi maka uzuri da shi daga abinda ka gabatar na ayyuka a duniya? daga kasancewarsa rafkanuwa ne, ko kuskurene ko jahilcine, Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji ba ni da wani hanzari. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Eh, lallai kana da wani kyakkyawan aiki a wurinMu, kuma cewa babu wani zalinci akanka a yau. Ya ce: Sai a fitar da wani kati an rubutawa a ciki: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: ka zo wurin ma’aunin ka. Sai mutumin ya ce, yana mai mamaki; Ya Ubangiji! Menene nauyin wannan katin tare da wadannan fayilill din ??. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Wani zalinci ba zai afku akanka ba. Sai ya ce ; sai a dora fayilillikan a ma'aunin, katin ma a daya ma'aunin; sai ma'aunin da fayilillkan suke a ciki su yi sauki, sai ma'aunin da katin yake ciki ya rinjaya, kuma ya yi nauyi, sai Allah Ya gafarta masa.