Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .
+ -

عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عنه قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ مَا آنِيَةُ الْحَوْضِ؟ قَالَ: «وَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَآنِيَتُهُ أَكْثَرُ مِنْ عَدَدِ نُجُومِ السَّمَاءِ وَكَوَاكِبِهَا، أَلَا فِي اللَّيْلَةِ الْمُظْلِمَةِ الْمُصْحِيَةِ، آنِيَةُ الْجَنَّةِ مَنْ شَرِبَ مِنْهَا لَمْ يَظْمَأْ آخِرَ مَا عَلَيْهِ، يَشْخَبُ فِيهِ مِيزَابَانِ مِنَ الْجَنَّةِ، مَنْ شَرِبَ مِنْهُ لَمْ يَظْمَأْ، عَرْضُهُ مِثْلُ طُولِهِ، مَا بَيْنَ عَمَّانَ إِلَى أَيْلَةَ، مَاؤُهُ أَشَدُّ بَيَاضًا مِنَ اللَّبَنِ، وَأَحْلَى مِنَ الْعَسَلِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2300]
المزيــد ...

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ce: Ya Manzon Allah menene kofunan tafki? (Sai) ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, kofunansa sun fi yawan adadin taurarin sama ku saurara a cikin duhun daren da babu hazo, kofunan Aljanna wanda ya sha daga garesu ba zai yi kishirwa ba har karshen al’amarinsa (na kishirwa), indararo biyu ne suke zuba a cikinsa daga Aljanna, wanda ya sha daga gareshi Ba zai yi kishirwa ba, fadinsa tamkar tsawonsa ne, tsakanin Amman zuwa Ailata, ruwansa ya fi nono tsananin fari, kuma ya fi zuma zaki".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2300]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan cewa kofunan tafkinsa a ranar Alkiyama sun fi yawan adadin taurarin sama, Wannan yana bayyana a cikin dare mai duhun da babu wata a cikinsa; domin kuwa dare mai wata taurari ba sa kasancewa a bayyane a cikinsa dan boyuwarsu da hasken wata, kuma wacce babu hazo a cikinta; domin samun hazo yana hana ganin taurari, Kuma cewa kofunan Aljanna, wanda ya sha daga abin shan dake cikin su ba zai yi kishirwa ba har abada, kuma wannan yana kasancewa karshen abinda yake samun mai shan na kishirwa. Kuma cewa tafkinsa indararo biyu daga Aljanna suna zuba a cikinsa, kuma fadinsa tamkar tsawonsa ne; Tafkin madaidaicin rukunai ne, tsawonsa yana kasancewa gwargwadan tazarar dake tsakanin Amman -ita wani gari ne a Balka'a daga Sham-, zuwa Ailata, wani birni ne sananne a gefen Sham. Ruwan tafkin ya fi nono fari, kuma dandanonsa ya fi zuma zaki.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tabbatar da tafki da abinda ke cikinsa na nau'o'in ni'ima.
  2. Girman tafkin da tsawonsa da fadinsa da yawan kofunan sa.