Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .
+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَلاَ أُحَدِّثُكُمْ حَدِيثًا عَنِ الدَّجَّالِ، مَا حَدَّثَ بِهِ نَبِيٌّ قَوْمَهُ؟ إِنَّهُ أَعْوَرُ، وَإِنَّهُ يَجِيءُ مَعَهُ بِمِثَالِ الجَنَّةِ وَالنَّارِ، فَالَّتِي يَقُولُ إِنَّهَا الجَنَّةُ هِيَ النَّارُ، وَإِنِّي أُنْذِرُكُمْ كَمَا أَنْذَرَ بِهِ نُوحٌ قَوْمَهُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3338]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta, wacce zai ce ita ce aljanna to ita ce wuta, lallai ni ina gargaɗarku kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗi al'ummarsa da shi".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3338]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da Dajjal da siffofinsa da almominsa da abinda wani annabi a gabaninsa bai zantar da shi ba, daga hakan:
Cewa shi mai ido ɗaya ne.
Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya masa kwatankwacin aljanna da wuta, gwargwdan ganin ido.
Sai dai aljannarsa wuta ce, kuma wutarsa aljanna ce, wanda ya bi shi zai shigar da shi wannan aljannar a abinda mutane suke gani, sai dai cewa ita wuta ce mai ƙuna, wanda ya saɓa masa zai shigar da shi wutar a abinda mutane suke ganinsa, sai dai ita aljanna ce mai daɗi. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga fitinarsa kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗar da mutanensa shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girman fitinar Dujal.
  2. Tsira daga fitinar Dajjal tana kasancewa ne da gaskiyar imani da fakewa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da neman tsari da Allah daga gare shi a tahiyar ƙarshe, da haddace ayoyi goma daga farkon surar Kahfi.
  3. Tsananin kwaɗayin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, lokacin da ya bayyanawa musulmai siffofin Jujal abinda wani annabi kafin shi bai bayyana shi ba.