عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَسْرِعُوا بِالْجِنَازَةِ، فَإِنْ تَكُ صَالِحَةً فَخَيْرٌ تُقَدِّمُونَهَا، وَإِنْ يَكُ سِوَى ذَلِكَ، فَشَرٌّ تَضَعُونَهُ عَنْ رِقَابِكُمْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1315]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1315]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yin gaggawa da shirya jana'iza da yi mata sallah da kuma binneta; idan jana'izar ta kasance ta garice to alheri ne, kuke gabatarwa gare shi na ni'imar ƙabari, idan kuma ta kasance koma bayan haka ne to sharri ne kuke saukewa daga wuyayenku.