عن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ شهدَ الْجَنَازَةَ حتى يصلَّى عليها فله قِيرَاطٌ، ومن شهدها حتى تُدفن فله قِيرَاطان، قيل: وما القِيرَاطَانِ؟ قال: مثل الجبلين العظيمين». ولمسلم: «أصغرهما مثل أُحُدٍ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

an karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi an daga hadisin zuwa ga Annabi: "wanda ya halarci Gawa har akai mata salla yana da kiradi guda.wanda kuma ya halarce ta har aka binneta yana da kiradi biyu.sai aka ce: menene kiradi biyu? sai yace: kwatankwacin manyan dutsuna biyu" a wata ruwayar kuma: "mafi kankantarsu kwatankwacin dutsen Uhudu"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Allah mai madaukakin suna da albarka mai tausasawa ne ga bayinsa, sa`annan yana nufin da ya shimfida musu dalilan yin gafara a garesu, musamman ma lokacin da zasu bar duniya, wadda ta ke ita ce gidan aiki, izuwa gidan da za`a ninke takardun ayyukan su a cikin ta. don hakanan ne ya kwadaitar bisa yin sallar jana`iza da halartar ta, saboda ita sallar neman ceto ne ga mamaci kuma tana kasancewa dalilin samun rahamar Allah. sai ya sanya ladan qiradi ga wanda ya sallace ta, ya kuma sanya wani ladan qiradin ga wanda ya halarci binne ta. wannan wani gwargwado ne daga lada mai girma kuma matsayinsa sananne ne wurin Allah madaukakin saki. yayin da gwargwadon girman wannan lada ya buya ga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su- sai Annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kusanto da shi ga kwakwalen su, ta yadda kowane qiradi ya kai girman babban dutse; saboda abinda ke ciki na girma tsayawa akan hakkin dan uwansa musulmi tare da yin addu`ah a gareshi da tunatarwa dangane da makoma da debewa mutanen gidan kewar mamacin su da wanin haka da maslahohi.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin