عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: «نَعَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم النَّجَاشِيَّ في اليوم الذي مات فيه، خرج بهم إلى المصلَّى، فصفَّ بهم، وكَبَّرَ أَرْبَعاً».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Annabi mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi ya bada labarin rasuwar Najjashi a cikin ranar da ya rasu, sai ya fito da su zuwa wurin sallah, sai ya yi sahu da su, ya yi kabbarori guda hudu
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annajjashi sarkin Habasha yana da babbar gudunmawa akan wadanda sukayi hijira zuwa kasarsa daga cikin sahabbai, a lokacin da quraishwa suka takura musu a garin makkah,kafin musuluntar mutanen madina sai ya girmama su, sa`annan kyakkyawar niyyar sa da bin gaskiyar sa, da kuma korewa kansa girman kai, suka kaishi ga shiga addinin musulunchi, sai ya rasu a kasar sa, alhalin bai hadu da Annabi ba saboda kyautatawarsa ga musulmai, da girman matsayin sa da kasancewar sa yana wata kasa da ba`ayi masa sallaha cikinta ba, sai manzon Allah mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi ya baiwa sahabban sa labarin rasuwar Najjashi a ranar da ya rasu a cikinta, sai ya fita da su zuwa wurin yin sallah saboda kambama sha`anin Najjashi don kuma ya bayyanawa sahabban sa cewa ya musulunta da sanar musu da falalar sa da kuma yi masa sakayya gameda abinda ya yiwa masu masu Hijira, da neman yawaitar masu yi masa sallah, sai Annabi ya yi musu sahu sahu ya yi masa sallar gaa`ibi ya yi kabbarori guda hudu a cikin wannan sallar, don neman ceto a gareshi a wajen Allah madaukakin sarki

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin