عن عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ:
«مَنْ جَاءَ مِنْكُمُ الْجُمُعَةَ فَلْيَغْتَسِلْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 894]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 894]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ƙarfafa cewa wanda ya yi nufin zuwa sallar Juma'a to an so gareshi ya yi wanka, kamar irin wankansa na janaba.