عَنِ الْبَرَاءِ بْنِ عَازِبٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
أَمَرَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِسَبْعٍ، وَنَهَانَا عَنْ سَبْعٍ: أَمَرَنَا بِعِيَادَةِ الْمَرِيضِ، وَاتِّبَاعِ الْجَنَازَةِ، وَتَشْمِيتِ الْعَاطِسِ، وَإِبْرَارِ الْقَسَمِ، أَوِ الْمُقْسِمِ، وَنَصْرِ الْمَظْلُومِ، وَإِجَابَةِ الدَّاعِي، وَإِفْشَاءِ السَّلَامِ، وَنَهَانَا عَنْ خَوَاتِيمَ -أَوْ عَنْ تَخَتُّمٍ- بِالذَّهَبِ، وَعَنْ شُرْبٍ بِالْفِضَّةِ، وَعَنِ الْمَيَاثِرِ، وَعَنِ الْقَسِّيِّ، وَعَنْ لُبْسِ الْحَرِيرِ وَالْإِسْتَبْرَقِ وَالدِّيبَاجِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2066]
المزيــد ...
Daga Bara’u ɗan Azib -Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai: Ya umarcemu da duba mara lafiya, da raka jana’iza, da gaida mai atishawa, da kuma kuɓutar da rantsuwa, ko mai rantsuwa, da taimakon wanda aka zalunta, da kuma amsawa mai gayyata, da yaɗa sallama.
Ya kuma hana mu yin zobe - ko sanya zoben zinare, da sha acikin abin sha na azurfa, da al-Mayathir, (Shi ne matakalar abunda ake sanyawa a shinfidar doki) da al-ƙissi (zabon Masar, nau’i ne na alhariri mai kauri) da kuma sanya alharini, da al-Istabraƙ (Alharini mai kauri) Dibaj (shi ma nau’i ne na alharini mai kauri).
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2066]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmai da ɗabi'u bakwai kuma ya hanesu ɗabi'u bakwai; waɗanda ya umarce su sune: Na farkonsu: Ziyarar mara lafiya. Na biyunsu: Raka jana'iza da tarayya ta hanyar yi mata sallah da kuma binneta, da yi mata addu'a. Na ukunsu: Yin addu'a ga wanda ya yi atishawa kuma ya godewa Allah, shi ne ace masa: Allah Ya yi maka rahama. Na huɗunsu: Kuɓutar da mai rantsuwa da kuma gasgata shi, ma'ana cewa da zai yi rantsuwa akan wani al'amari alhali kai kana da iko akan sanya shi kuɓutacce a cikinta to ka aikata; dan kada ka bar shi zuwa yin kaffara ta rantsuwar. Na biyarɗinsu: Taimakon wanda aka zalinta, ta hanyar taimaka masa da tunkuɗe abinda yake afka masa daga azzalimi gwargwadan iko. Na shidansu: Amsa gayyata zuwa walimar abin ci, kamar walimar angwanci, ko suna, ko waninsu. Na bakwansu: Yin sallama da yaɗata da kuma amsata. Waɗanda kuma ya hanasu su ne: Na farkonsu: Sanya zobunan zinare da kuma yin ado da su. Na biyunsu: Shan abu a ƙwaryar azirfa. Na ukunsu: Zama akan Mayasir, sune shimfiɗun da ake sawa akan sirdin doki da kuma sirdin raƙumi na alharaini. Na huɗunsu: Sanya tufafin da aka yi da kattanin da aka cakuɗa da alharini kuma ana ambatansa: (Alƙisiyyu). Na biyarɗinsu: Sanya alharaini. Na shidansu: Sanya Istabraƙ, shi ne: Alharini mai kauri. Na bakwansu: Sanya Dibaj, shi ne: Mafi kyan nau'ikan alharini kuma mafi tsadarsu.