عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بن مسعودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِنَّ مِنْ شِرَارِ النَّاسِ مَنْ تُدْرِكُهُ السَّاعَةُ وَهُمْ أَحْيَاءٌ، وَمَنْ يَتَّخِذُ الْقُبُورَ مَسَاجِدَ».

[حسن] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 3844]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa:
"Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai".

[Hasan ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [Musnad Ahmad - 3844]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da mafi sharrin mutane, cewa sune wadanda alkiyama zata tsaya akansu alhali su suna raye, da wadanda suke daukar kaburbura masallatai, suna sallah a wurinsu suna kuma kallonsu..

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin gina masallatai akan kaburbura; domin hakan hanyace zuwa ga shirka.
  2. Haramcin sallah a wurin kaburbura koda ba tare da gini ba; domin masallaci suna ne ga abinda ake sujjada a cikinsa koda babu gini a wurin.
  3. Wanda ya riki kaburburan salihai masallatai dan yin sallah a wurin to shi yana daga mafi sharrin mutane, koda ya yi ikirarin cewa manufarsa neman kusanci zuwa ga Allah - Madaukakin sarki -.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (56)