عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنَ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلَالَةٍ كَانَ عَلَيْهِ مِنَ الْإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ آثَامِهِمْ شَيْئًا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2674]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba, wanda ya yi kira zuwa ga bata yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga zunubansu ba".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2674]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya shiryar ya kwadaitar da mutane kan hanyar da aciknta akwai gaskiya da alheri da fada ne ko aikatawa yana da ladan wanda ya bi shi ba tare da antauye komai daga ladan mai bin ba. Wanda ya kira mutane zuwa hanyar karya da sharri a cikinta akwai zunubi da kuskure ko wani al'amarin da ba ya halatta, na fadane ko aikatawa, ya kasance akwai zunubi akansa kwatankwacin zunubin wanda ya bi shi ba tare da an tauye komai daga zunubansu ba.