عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ فِيهِ فَهُوَ رَدٌّ» متفق عليه.
ولمسلم: «مَنْ عَمِلَ عَمَلًا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2697]
المزيــد ...
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya farar da (wani abu) daga al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa". Daga Muslim: "Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya kan al'amarinmu to shi abin an mayar masa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2697]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.