عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «مَنْ تَابَ قَبْلَ أَنْ تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا تَابَ اللهُ عَلَيْهِ».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...
Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: "Duk wanda ya tuba kafin rana ta fito daga faduwarta, Allah zai tuba a kansa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]
Hadisin ya nuna cewa Allah mai girma da daukaka yana karbar tuba daga bawansa mai zunubi matukar dai rana ba ta fito daga yamma ba. Domin shine karshen lokacin karbar tuba kuma yana daga cikin manyan alamomin tashin kiyama.