عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا نَفَّسَ اللهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى مُعْسِرٍ يَسَّرَ اللهُ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَاللهُ فِي عَوْنِ الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِي عَوْنِ أَخِيهِ، وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا سَهَّلَ اللهُ لَهُ بِهِ طَرِيقًا إِلَى الْجَنَّةِ، وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللهِ يَتْلُونَ كِتَابَ اللهِ وَيَتَدَارَسُونَهُ بَيْنَهُمْ إِلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمِ السَّكِينَةُ، وَغَشِيَتْهُمُ الرَّحْمَةُ، وَحَفَّتْهُمُ الْمَلَائِكَةُ، وَذَكَرَهُمُ اللهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ، وَمَنْ بَطَّأَ بِهِ عَمَلُهُ لَمْ يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2699]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2699]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sakamakon musulmi a wurin Allah yana daga jinsin abinda musulmi yake aikata shi tare da musulmai; wanda ya yaye ya gusar ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki da tsanani daga baƙƙan cikin duniya, Allah Zai yi masa sakayya da cewa Zai Yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar alƙiyama. Wanda ya yalwatawa wanda ke ciki matsi ya kuma sawwaƙa masa ya gusar da matsinsa, Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira. Wanda ya suturta wani musulmi kamar idan ya tsinkaya daga gare shi akan abinda bayyanar da shi ba ya kamata na tuntuɓe da kurakurai, Allah Zai suturta shi a duniya da lahira. Allah Yana kasancewa Mai taimako ga bawanSa, muddin dai bawan ya kasance mai tafiya ne akan taimakon ɗan uwansa a maslahohinsa na Addini da duniya, taimako yana kasancewa ne da addu'a da jiki da dukiya da kuma wanin hakan. Wanda ya yi tafiya zuwa tabbatar da wani ilimi na shari'a, yana mai nufin fuskar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi; to Allah Zai sawwaƙa masa hanya zuwa aljanna da shi. Wasu mutane ba su taru ba a wani ɗaki daga ɗakunan Allah, suna karanta littafin Allah kuma suna mudarasarsa a tsakaninsu, sai nutsuwa ta saukar musu, rahamar Allah ta gamesu ta lulluɓesu, kuma mala'iku sun kewayesu, Allah Ya yi yabo a garesu a cikin makusantan dake wajenSa, kuma ambatan Allah ga bawa a cikin jama'a maɗaukaka ya isa ɗaukaka. Wanda aikinsa ya kasance tauyayye ne, Ba zai riskar da shi da darajar ma'abota ayyuka ba, to yana kamata kada ya dogara akan ɗaukakar nasaba da falalar iyaye, ya taƙaita a cikin aiki.