عَنْ أُمِّ المُؤْمِنِينَ أُمِّ عَبْدِ اللَّهِ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ: قَالَ: رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم:
«مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ مِنْهُ فَهُوَ رَدٌّ».
وَفِي رِوَايَةٍ لِمُسْلِمٍ: «مَنْ عَمِلَ عَمَلًا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ».
[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية: 5]
المزيــد ...
Daga uwar muminai Babar Abdullahi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, ta ce: Manzon Allah - tsira amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne».
[Ingantacce ne] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية - 5]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.