Karkasawa:
+ -

عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
حَدَّثَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ الصَّادِقُ المَصْدُوقُ: «إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا، ثُمَّ يَكُونُ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ إلَيْهِ المَلَكُ فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ: بِكَتْبِ رِزْقِهِ، وَأَجَلِهِ، وَعَمَلِهِ، وَشَقِيٍّ أَوْ سَعِيدٍ؛ فَوَالَّذِي لَا إلَهَ غَيْرُهُ إنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الجَنَّةِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ فَيَدْخُلُهَا، وَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الجَنَّةِ فَيَدْخُلُهَا».

[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية: 4]
المزيــد ...

Daga Abu Abdurrahman Abdullahi ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya karantar da mu alhali shi mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa: «Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in yana maniyyi, sannan ya zama gudan jini misalin haka, sannan ya zama gudan tsoka misalin haka, sannan a aiko masa da mala’ika sai ya busa masa rai, kuma a umarce shi da kalmomi guda huɗu: Da rubuta arziƙinsa, da ajalinsa, da aikinsa, kuma shi ɗan wuta ne ko ɗan aljanna ne, na rantse da wanda babu wani abin bautawa da cancanta in ba shi ba, lallai ɗayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta sai zira’i, sai littafi ya rigaya a kansa, sai ya yi aiki aiki irin na 'yan wuta sai ya shige ta, kuma cewa ɗayanku zai yi aiki aiki irin na 'yan wuta har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta sai dai zira’i sai littafi ya rigaya a kansa, sai ya yi aiki aiki irin na 'yan aljannah sai ya shige ta».

[Ingantacce ne] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية - 4]

Bayani

Dan Mas'ud ya ce:: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiyane a zancensa, kuma abin gasgatawa yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya gasgata shi. Ya ce: Lallai cewa dayanku ana taro halittarsa, cewa mutum idan ya zo wa iyalansa to tarwatsettsen maniyyinsa ana taroshi a cikin mace kwana arba'in yana maniyyi. Sannan ya zama gudan jini ita ce gudan jini mai kauri sandararre, wannan a arba'in ta biyu ne, Sannan ya zama gudan tsoka ita ce yanki na nama gwargwadan abinda ake taunawa, wannan a arba'in ta uku ce, Sannan sai Allah Ya aiko masa da Mala'ika, sai ya busa rai a cikinsa bayan karewar arba'in ta uku, Sai a umarci Mala'ikan da ya rubuta kalmomi hudu su ne: Arzikinsa, shi ne gwargwadan abin da zai samu daga ni'imomi a rayuwarsa, Da ajalinsa, shi ne gwargwadan wanzuwarsa a duniya, Da aikinsa, menene shi? dan wutan ne ko dan Aljanna ne. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa cewa; mutum zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna kuma aikinsa zai zama na gari, wato a abinda yake bayyana ga mutane, kuma ba zai gushe a haka ba har ya kasance tsakaninsa da ita bai zama ba sai zira'i daya, wato: Babu abinda zai wanzu tsakaninsa da tsakanin saduwa da ita aljannar sai kamar wanda zai zama tsakaninsa da tsakanin wani wuri na kasa zira'i daya ne, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa to a wannan lokacin zai yi aiki da aikin 'yan wuta sai a cika masa da shi sai ya shiga wutar; Domin cewa sharadin karbar aikinsa shi ne ya tabbata akansa ta yadda ba zai canjaba, wani dayan kuma daga mutane zai yi ayyukan 'yan wuta har sai ya kusanci shigarta, kuma gwargwadan zira'i ne na kasa zai kasance tsakakninsa da wutar, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa, sai ya yi aikin 'yan Aljanna kuma ya shiga Aljannar.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin matakan halittar mutum.
  2. Yin imani da hukuncin (Allah) da kuma ƙaddara.
  3. Makomar al'amura a karshe zuwa ga abinda hukunci ya rigaya da shi ne, kuma kaddara ta gudana da shi.
  4. Gargadi akan ruduwa da yanayin ayyuka; kadai ayyuka da karshe ne kawai.
  5. ____
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci الأمهرية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda المجرية التشيكية الموري Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari