عن ابن عباس رضي الله عنهما أنه رأى رجلا انْتَفَضَ لما سمع حديثا عن النبي صلى الله عليه وسلم في الصفات -استنكارا لذلك– فقال: "ما فَرَقُ هؤلاء؟ يجدون رِقَّةً عند مُحْكَمِهِ، ويَهْلِكُونَ عند مُتَشَابِهِهِ" .
[صحيح] - [رواه عبد الرزاق وابن أبي عاصم]
المزيــد ...
Daga Dan Abbas -Allah ya yarda dasu-ya ga wani mutum ya firgita yayin da yaji wani hadisi game da Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- game da sifofin Allah-don nuna rashin yardarsa da haka- sai yace: Meye banbancin wadannan?zuciyarsu na yin taushi in suka ji ayoyi bayyanannu,su kuma rikice in suka ji ayoyi masu rikitarwa".
[Ingantacce ne] - [Ibnu Abi Asim ya rawaito shi - Abdurrazak Ya Rawaito shi]
Ibn Abbas -Allah ya yarda dasu- ya tsani duk mai tsorata a dalilin ya ji hadisai da suke magana akan siffofinAllah har ma su razana don kin abin,ba sa imani da abin da ya zo daga manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- wanda suka san ma'anarsa daga Alkur'ani wanda shi ne gaskiya, mumini ba ya kokwanto a cikinsa, wasa kuma sai suke daukarsa ba a ma'anarsa da Allah yake nufi ba sai su halaka a dalilinhaka