Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .
+ -

عَنْ أَسْمَاءَ بِنْتِ أَبِي بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَتْ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنِّي عَلَى الحَوْضِ حَتَّى أَنْظُرَ مَنْ يَرِدُ عَلَيَّ مِنْكُمْ، وَسَيُؤْخَذُ نَاسٌ دُونِي، فَأَقُولُ: يَا رَبِّ مِنِّي وَمِنْ أُمَّتِي، فَيُقَالُ: هَلْ شَعَرْتَ مَا عَمِلُوا بَعْدَكَ، وَاللَّهِ مَا بَرِحُوا يَرْجِعُونَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6593]
المزيــد ...

Daga Asma'u bint AbuBakar - Allah Ya yarda da su - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne, sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata a bayanka, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan digadigensu".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6593]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa shi zai kasance a ranar Alkiyama akan tafkinsa dan ya ga wanda zai zo daga al'ummarsa zuwa tafkin, Kuma za'a rike wasu mutane a kusa da shi - aminci ya tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Ubangiji daga gareni ne kuma daga al'ummata ne, Sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata bayan rabuwarka da su, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan bayansu suna yin ridda daga addininsu, su ba sa tare da kai, kuma ba sa cikin al'ummarka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rahamar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kwadayinsa gare su .
  2. Hadarin sabawa abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa.
  3. Kwadaitarwa akan riko da sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.