عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما قَالَ: قالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«حَوْضِي مَسِيرَةُ شَهْرٍ، مَاؤُهُ أَبْيَضُ مِنَ اللَّبَنِ، وَرِيحُهُ أَطْيَبُ مِنَ المِسْكِ، وَكِيزَانُهُ كَنُجُومِ السَّمَاءِ، مَنْ شَرِبَ مِنْهَا فَلاَ يَظْمَأُ أَبَدًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6579]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi, kofunansa kamar taurarin sama ne, wanda ya sha daga gare shi ba zai yi kishirwa ba har abada".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6579]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa yana da wani tafki a ranar Alkiyama, tsawonsa tafiyar wata ne kuma fadinsama kamar haka ne. Kuma lallai cewa ruwansa ya fi nono tsananin fari. Kuma cewa kamshinsa mai dadi ne ya fi kamshin almiski. Kuma kofinansa tamkar taurarin sama ne a yawansu, Wanda ya sha daga tafkin da wadancan kofinan ba zai yi kishirwa ba har abada.