عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«المُسْلِمُ مَنْ سَلِمَ المُسْلِمُونَ مِنْ لِسَانِهِ وَيَدِهِ، وَالمُهَاجِرُ مَنْ هَجَرَ مَا نَهَى اللَّهُ عَنْهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 10]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 10]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.