عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا مِنْ نَبِيٍّ بَعَثَهُ اللهُ فِي أُمَّةٍ قَبْلِي إِلَّا كَانَ لَهُ مِنْ أُمَّتِهِ حَوَارِيُّونَ، وَأَصْحَابٌ يَأْخُذُونَ بِسُنَّتِهِ وَيَقْتَدُونَ بِأَمْرِهِ، ثُمَّ إِنَّهَا تَخْلُفُ مِنْ بَعْدِهِمْ خُلُوفٌ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ، وَيَفْعَلُونَ مَا لَا يُؤْمَرُونَ، فَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِيَدِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِلِسَانِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِقَلْبِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَلَيْسَ وَرَاءَ ذَلِكَ مِنَ الْإِيمَانِ حَبَّةُ خَرْدَلٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 50]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi, sannan wasu masu sabawa zasu saba a bayansu suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umarce su ba, wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi muminin ne, kuma babu wani kwatankwacin kwayar komayya na imani bayan hakan".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 50]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.