+ -

عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ أُمِّ المُؤمنين رضي الله عنها: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«سَتَكُونُ أُمَرَاءُ فَتَعْرِفُونَ وَتُنْكِرُونَ، فَمَنْ عَرَفَ بَرِئَ، وَمَنْ أَنْكَرَ سَلِمَ، وَلَكِنْ مَنْ رَضِيَ وَتَابَعَ» قَالُوا: أَفَلَا نُقَاتِلُهُمْ؟ قَالَ: «لَا، مَا صَلَّوْا».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1854]
المزيــد ...

Daga Ummu Salalmah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Za'a samu wasu shugabanni zaku sansu kuma zaku yi inkarinsu, wanda ya sani ya kubuta, wanda kuma ya yi inkari ya kubuta, saidai wanda ya yarda ya kuma bi" suka ce: Shin ba ma yakesu ba? ya ce: "A'a, muddin dai suna sallah".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1854]

Bayani

Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a shugabantar da wasu shugabanni akanmu, zamu san wasu daga ayyukansu; dan dacewarsu da abinda aka sani na shari'a, kuma zamu yi inkarin wasu ayyukan na su; dan sabawarsu ga hakan, Wanda ya ki da zuciyarsa amma ba shi da iko akan inkari; to hakika ya kubuta daga zunubi da kuma munafunci, Wanda ya samu iko akan inkari da hannu ko da harshe sai ya yi inkarin hakan akansu to hakika ya kubuta daga sabo da kuma tarayya a cikinsu, sai dai wanda ya yarda da aikinsu ya kuma bi su akansa zai halaka kamar yadda suka halaka.
Sannan suka tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin ba ba ma yaki shugabannin da wannan ita ce siffarsu ba? mu hanasu hakan, sai ya ce: A'a, muddin dai sun tsaida sallah a cikinku.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Yana daga dalilan Annabcin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -yadda ya bada labari game da abinda zai auku na gaibu da kuma afkuwarsa kamar yadda ya bada labarin.
  2. Yarda da abin ki ba ya halatta ko tarayya a cikinsa, kuma inkarinsa yana wajaba.
  3. Idan shugabani suka farar da abinda ya sabawa shari'a to yi musu biyayya a kan hakan bai halatta ba.
  4. Rashin halaccin tawaye ga shugabannin musulmai; dan abinda yake biyo baya na barna da zubar da jini da rashin amincin akan hakan, to jurewar mai inkarin shugabanni, da hakuri akan cutar Warshu shi ne mafi sauki daga yi musu tawaye.
  5. Sallah al'amarinta mai girma ne, ita ce mai banbantawa tsakanin kafirci da musulunci.