عن عرفجة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«مَنْ أَتَاكُمْ وَأَمْرُكُمْ جَمِيعٌ عَلَى رَجُلٍ وَاحِدٍ، يُرِيدُ أَنْ يَشُقَّ عَصَاكُمْ، أَوْ يُفَرِّقَ جَمَاعَتَكُمْ، فَاقْتُلُوهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1852]
المزيــد ...
Daga Arfajah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi ".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1852]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa musulmai idan suka haɗu a kan shugabancin mutum ɗaya, da jama'a ɗaya, sannan wani ya zo yana son ya yi jayayya da shi a shugabanci, ko yana son raba musulmai sama da kungiya ɗaya, to, ya wajaba su hana shi da kuma yaƙarsa; don tunkuɗe sharrinsa da kuma kare jinanen musulmai.