+ -

عَنْ عِكْرِمَةَ:
أَنَّ عَلِيًّا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ حَرَّقَ قَوْمًا، فَبَلَغَ ابْنَ عَبَّاسٍ فَقَالَ: لَوْ كُنْتُ أَنَا لَمْ أُحَرِّقْهُمْ لِأَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تُعَذِّبُوا بِعَذَابِ اللَّهِ»، وَلَقَتَلْتُهُمْ كَمَا قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 3017]
المزيــد ...

Daga Ikramah:
Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi».

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3017]

Bayani

Aliyu ibnu Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi ijtihadi sai ya ƙona wasu mutane daga cikin zindiƙai waɗanda suka yi ridda suka bar Musulunci (ya Kona su) da wuta, sai labarin hakan ya kai ga Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, sai ya ƙarfafe shi akan kisan su; sai dai ya yi inkarin ƙona su da wuta. Kuma ya ce: Da ace nine a matsayinsa da ban ƙonasu da wuta ba; domin shi Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu mai yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta, saidai kashesu ya wadatar, inda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk wanda ya yi ridda daga Musulunci ya canja Addinisa zuwa wani Addinin daban to ku kashe shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin kashe wanda ya yi ridda ya bar Musulunci da ijma'in ma'abota ilimi, hakan da sharuɗɗansa, bamai aikata haka sai shugaba da alƙali.
  2. Faɗinsa: "Wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi" wato: Wanda ya yi ridda daga Musulunci: Hukunci ne gamamme ga maza da mata.
  3. Wanda ya yi ridda ba'a barinsa akan riddarsa, kai za'a kira shi zuwa ga Musulunci, idan bai amsa ba sai a kashe shi.
  4. A cikin wannan hadisin akwai hani akan azabtarwa da wuta, kuma haddodi ba'a zartar da su da wuta.
  5. Falalar Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, da yalwar iliminsa da fahimtarsa da hadisan Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  6. A cikin wannan akwai ladabin inkari akan wanda ya saɓa.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin