عَنْ أَبِي ذَرٍّ، جُنْدُبِ بْنِ جُنَادَةَ، وَأَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ، مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«اتَّقِ اللَّهَ حَيْثُمَا كُنْت، وَأَتْبِعْ السَّيِّئَةَ الْحَسَنَةَ تَمْحُهَا، وَخَالِقْ النَّاسَ بِخُلُقٍ حَسَنٍ».
[قال الترمذي: حديث حسن] - [رواه الترمذي] - [الأربعون النووية: 18]
المزيــد ...
Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».
[قال الترمذي: حديث حسن] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [الأربعون النووية - 18]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.