عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَمَا يَخْشَى أَحَدُكُمْ - أَوْ: لاَ يَخْشَى أَحَدُكُمْ - إِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ قَبْلَ الإِمَامِ، أَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ رَأْسَهُ رَأْسَ حِمَارٍ، أَوْ يَجْعَلَ اللَّهُ صُورَتَهُ صُورَةَ حِمَارٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 691]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 691]
Annabi - - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana narko mai tsanani akan wanda ya dago kansa kafin limaminsa, Allah Ya maida kansa kan jaki, ko Ya maida surar halittarsa ta zama surar jaki.