عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«سَوُّوا صُفُوفَكُمْ، فَإِنَّ تَسْوِيَةَ الصَّفِّ مِنْ تَمَامِ الصَّلَاةِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 433]
المزيــد ...
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 433]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar masu yin sallah kan su daidaita sahunsu, kuma kada sashinsu ya gabata akan sashi kada kuma ya jinkirta, kuma daidaita sahu yana daga cikar sallah , kuma karkace sahu ɓaci ne da tawaya a sallah.