عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «إنما جُعِلَ الإمام ليِؤُتَمَّ به، فلا تختلفوا عليه، فإذا كبر فكبروا، وإذا ركع فاركعوا، وإذا قال: سمع الله لمن حمده، فقولوا: ربنا ولك الحمد. وإذا سجد فاسجدوا، وإذا صلى جالسا فصلوا جلوسا أجمعون».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira -Allah yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Kuma ai ansanya Limami ne don ayi koyi da shi, to kuma kada ku saba Masa, to idan yayi kabbara to kuyi kabbara, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i, kuma idan yace Allah yaji mai gode masa,to ku ce: Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareka, kuma idan yayi Sujada to kuyi Sujada, kuma idan yai Sallah a zaune to kuyi sallah kuma a a zaune baki dayanku"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya shiryar da mamu izuwa Hikimar da ta sa aka sanya Limami kuma ita ce cewa duk wanda ya bishi Sallah to yayi koyi da shi a Sallarsa, kuma kada ya saba Masa da wani aiki na ayyukan Sallah, kuma ya kula da duk motsinsa a tsare to idan yai kabbarar harama, to kuyi harama kuma, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i bayansa, kuma idan ya tunasar da ku cewa Allah yana amsa fadin wanda ya gode masa to ku godewa Allah da fadinku, kuma wata sigar ta zo daban kamar ya Ubangiji Ubangijinmu godiya a gareka, kuma idan yayi sujada to ku bishi kuma kuyi sujad, kuma idan yai sallah a zaune -sabida gajiyawa ga barin iya tsayiw- to sabida tabbatar da biyayya kuma kuyi sallah a zaune kuma koda zaku iya tsayiwa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin