عَنْ وَابِصَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَأَى رَجُلًا صَلَّى وَحْدَهُ خَلْفَ الصَّفِّ، فَأَمَرَهُ أَنْ يُعِيدَ صَلَاتَهُ.

[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [مسند أحمد: 18000]
المزيــد ...

Daga Wabisah - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallar.

[Hasan ne] - [Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi] - [Musnad Ahmad - 18000]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallarsa; domin sallarsa ba ta inganta ba a wannan halin.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan gaggawar zuwa sallar jam’i da halartarta, kuma kada ya yi sallah a bayan sawu shi kaɗai dan kada ya bijirar da sallarsa ga ɓaci.
  2. Ibnu Hajar ya ce: Wanda ya fara sallah shi kaɗai a bayan sawu sannan ya shiga cikin sawu kafin ɗagowa daga ruku'u to sakewa ba ta wajaba gare shi ba, kamar yadda yake a cikin hadisin Abu Bakrata, inba haka ba to yana wajaba abisa gamewar hadisin Wabisah.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (44)