عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«خَيْرُ صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا، وَشَرُّهَا آخِرُهَا، وَخَيْرُ صُفُوفِ النِّسَاءِ آخِرُهَا، وَشَرُّهَا أَوَّلُهَا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 440]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 440]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi alherin sahun maza a cikin sallah kuma mafi yawansu a lada da falala shi ne na farkonsu; dan kusancinsu ga liman da jinsu ga karatunsa da nisantarsu daga mata. Mafi sharrinsu kuma mafi ƙarancinsu a lada da falala, kuma mafi nisancinsu daga abin nema a shari'a shi ne ƙarshensu. Mafi alherin sahun mata na ƙarshensu; domin cewa yafi sutura garesu, kuma mafi nisanta daga cakuɗuwa da maza da ganinsu da fitinuwa da su, mafi sharrinsu na farkonsu; dan kusancinsu ga maza da bijirowa ga fitina.