عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ غَدَا إِلَى الْمَسْجِدِ أَوْ رَاحَ أَعَدَّ اللهُ لَهُ فِي الْجَنَّةِ نُزُلًا، كُلَّمَا غَدَا أَوْ رَاحَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 669]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
"Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 669]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya zo masallaci dan yin ibada ko ilimi ko wanin hakan daga manufofin alheri a kowanne lokaci albishir; a farkon yini ko ƙarshensa da cewa Allah haƙiƙa ya tanadar masa da wani wuri da garar baƙi a cikin aljanna, duk lokacin da ya zo masallaci a dare ko yini.