+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيَقُلْ خَيْرًا أَوْ لِيَصْمُتْ، وَمَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيُكْرِمْ جَارَهُ، وَمَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيُكْرِمْ ضَيْفَهُ».

[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce :
"Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa bawan da ya yi imani da Allah da ranar lahira wadda makomarsa take a cikinta, kuma a cikinta sakayyar aikinsa take, to, imaninsa zai kwaɗaitar da shi a kan aikata waɗannan ɗabi'un.
Na farko: Magana mai kyau: Ta tasbihi da hailala, da horo da aikin alheri, da hani daga abin ƙi, da gyara a tsakaknin mutane, idan bai aikata ba, to, ya lazimci shiru, ya kame daga cutarwa, ya kiyaye harshensa.
Na biyu: Girmama maƙoci: Da kyautata masa da rashin cutar da shi.
Na uku: Girmama baƙo mai gabatowa don ziyararka: Ta hanyar daddaɗan zance da ciyar da abinci da makamancin hakan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Imani da Allah da ranar lahira asali ne ga kowane alheri, kuma yana zaburarwa a kan aikin alheri.
  2. Gargaɗi daga illolin harshe.
  3. Addinin musulunci addinin sabo ne da karamci
  4. Waɗannan ɗabi'un suna daga yankin imani kuma daga ladubba ababen yabo.
  5. Yawaita zance zai iya kai wa zuwa abin ƙi ko abin haramtawa, kuɓuta tana cikin rashin magana sai ta alheri.