عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ كَانَتْ لَهُ مَظْلَمَةٌ لِأَخِيهِ مِنْ عِرْضِهِ أَوْ شَيْءٍ فَلْيَتَحَلَّلْهُ مِنْهُ اليَوْمَ، قَبْلَ أَلا يَكُونَ دِينَارٌ وَلاَ دِرْهَمٌ، إِنْ كَانَ لَهُ عَمَلٌ صَالِحٌ أُخِذَ مِنْهُ بِقَدْرِ مَظْلَمَتِهِ، وَإِلَمْ تَكُنْ لَهُ حَسَنَاتٌ أُخِذَ مِنْ سَيِّئَاتِ صَاحِبِهِ فَحُمِلَ عَلَيْهِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2449]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2449]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci dukkan wanda ya aikata wani zalinci ga ɗan'uwansa musulmi a mutunci ne, ko dukiya, ko jini ya nemi wanda ya zalinta ya yafe masa tunda yana duniya, tun kafin ranar lahira ta zo, inda dinari ko dirhami ba za su yi amfani ba ga wanda ya baiwa wanda ya zalinta ba, dan ya fanshi kansa da shi ba; domin sakayya a wannan ranar da kyawawan ayyuka ne da kuma munana. Inda wanda aka zalinta zai kwasa daga kyawawan ayyukan azzalimin gwargwdan zalincinsa, idan azzalimin ba shi da wasu kyawawan ayyuka sai a labtawa azzalimin munanan ayyukan wanda aka zalinta gwargwadan zalincin da ya yi.