عن جُندب بن عبد الله القَسْرِِي رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ صَلَّى صَلَاةَ الصُّبْحِ فَهُوَ فِي ذِمَّةِ اللهِ، فَلَا يَطْلُبَنَّكُمُ اللهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَيْءٍ، فَإِنَّهُ مَنْ يَطْلُبْهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَيْءٍ يُدْرِكْهُ، ثُمَّ يَكُبَّهُ عَلَى وَجْهِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ».

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Jundub ɗan Abbdullah AL Qasri- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah, Kada ku kuskura Allah Ya kamaku da wani (laifi) cikin alƙawarinsa; domin cewa duk wanda ya nemeshi da wani abu (na laifi) Zai kamashi, sannan Ya kifar da shi ta fuskarsa a cikin wutar Jahannama".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya sallaci Asuba, to, zai kasance cikin kiyayewar Allah da gadinsa da tsarinsa, kuma Zai yi kariya gareshi, kuma zai yi ɗauki gareshi.
Sannan (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya yi gargaɗi game da warware wannan alƙawarin da ɓatashi, ko dai da barin sallar Asuba, ko da bijirowa mai sallatarta da ta'addanci a kansa, to, duk wanda ya aikata haka to haƙiƙa ya keta wannan tsarin, kuma ya cancanci narko mai tsanani na cewa Allah Zai nemeshi saboda abin da ya yi sakaci na haƙƙinsa, wanda kuwa Allah Ya nemeshi Zai kamashi, sannan Ya jefashi a wuta ta fuskarsa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin muhimmancin (sallar) Asuba da falalarta.
  2. Gargaɗi mai tsanani game da bijirowa da mummunan (aiki) ga wanda ya sallaci Asuba.
  3. Kamun Allah - Maɗaukakin sarki - ga wanda yake bijirowa bayinsa na gari.