+ -

عَنْ جَرِيرِِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه قَالَ:
بَايَعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلاَةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، وَالنُّصْحِ لِكُلِّ مُسْلِمٍ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2157]
المزيــد ...

Daga Jariri Dan Abadullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi caffa - akan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ji da bi, da nasiha ga kowanne musulmi.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2157]

Bayani

Sahabi Jariru Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya dorawa kansa ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alkawari akan tauhidi, da yin salloli biyar a yini da dare, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu, da kuma bada zakka ta dole, ita ce ibada ta dukiya wajiba, ana karba daga mawadata ana bada ita ga macancanta daga talakawa da wasunsu, da kuma biyayya ga shugabanni, da nasiha ga kowanne musulmi, hakan ta hanyar kwadayi akan amfanar da shi, da sadar da alheri gare shi, da tunkude sharri daga gare shi ta hanyar magana da aikatawa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Muhimmancin sallah da zakka, su biyun suna daga rukunan Musulunci.
  2. Muhimmancin nasiha da yin nasiha tsakanin musulmai, har Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbai - Allah Ya yarda dasu - caffa akanta.