+ -

عن جابر بن عبد الله الأنصاري رضي الله عنهما قال: «كَانَ صلى الله عليه وسلم يُصَلِّي الظُّهْرَ بِالهَاجِرَة، والعَصرَ والشَّمسُ نَقِيَّة، والمَغرِب إِذَا وَجَبَت، والعِشَاء أَحيَانًا وأَحيَانًا: إِذَا رَآهُم اجتَمَعُوا عَجَّل، وَإِذَا رَآهُم أَبْطَئُوا أًخَّر، والصُّبحُ كان النبي صلى الله عليه وسلم يُصَلِّيهَا بِغَلَس».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir Dan Abdullah mutumin Madina -Allah ya yarda da su- yace: "Annabi tsira da amincin Allah ya kasance yana yin sallar Azahar a lokacin garjin rana, yakan sallaci La'asar lokaci da rana ta yi garau, Magariba kuma in rana ta fadi, Issha'i kuma wani lokacin ya ggaggauta yinta in ya ga an taru, wani likacin kuma ya jinkirta ta in yaga an makara, Asuba kuma ya kasance yana yin ta da sauran duhu"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Wannan hadisi yana nuni da lokacin da yafi a yi kowacce daga cikin salloli biyar,ka ga sallar Azahar:ana yin tane lokacin da rana ta karkata daga tsakkiya,shi ne lokacin zawali, shi ne farkon lokacinta.La'a sar kuma: ana yinta lokacin da rana take fara fat, ba wani fatsi-fatsi da ya gauraya da ita,yadda ake gane lokacinta shi ne tsawon komai ya lunka, Magariba kuma ana yinta ne lokacin faduwar rana da sanda ta buya. Issha'i kuma sai a kula da yanayin mutane in sun zo da wuri a farkon lokacinta,shi ne lokacin buyan jan shafaki to sai a yi ta, in kuma basu zo ba to sai a jinkirta ta har wajen tsakkiyar dare na farko, don shi ne lokacinta da ya fi ba don takurawa ba. amma Asuba shi ne farkon lokacin da haske ya fara dan bullowa

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin