عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ يُصَلِّي أَحَدُكُمْ فِي الثَّوْبِ الوَاحِدِ لَيْسَ عَلَى عَاتِقَيْهِ شَيْءٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 359]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 359]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi sallah a tufa ɗaya ya tsiraitar da kafaɗunsa abinda ke tsakanin kafaɗa da wuya ta inda kada, ya sarayar da wani abinda zai suturtasu; domin kafaɗu biyu duk da ba al'aura ba ne, to lallai suturtasu ya fi tabbata a ɓoye al'aura, kuma shi ne mafi kusanci zuwa girmama Allah - Maɗaukakin sarki - da girmamaShi a tsakiyar tsayuwa a gabanSa a cikin sallah.