+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بِن مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ:
سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ العَمَلِ أَحَبُّ إِلَى اللَّهِ؟ قَالَ: «الصَّلاَةُ عَلَى وَقْتِهَا»، قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ بِرُّ الوَالِدَيْنِ» قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ» قَالَ: حَدَّثَنِي بِهِنَّ، وَلَوِ اسْتَزَدْتُهُ لَزَادَنِي.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 527]
المزيــد ...

Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 527]

Bayani

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya.
Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Fifikon ayyuka a tsakaninsu gwargwadon yadda Allah yake son su .
  2. Kwadaitarwar muslmi akan kwadayi akan ayyuka mafifita sai mafifita.
  3. Fifikon amsawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafifitan ayyuka gwargwadan sabanin mutane da halayensu, da abinda yake mafi yawan amfani ga kowanne daya daga cikinsu.