عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها:
أَنَّ أُمَّ سَلَمَةَ ذَكَرَتْ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَنِيسَةً رَأَتْهَا بِأَرْضِ الْحَبَشَةِ، يُقَالُ لَهَا مَارِيَةُ، فَذَكَرَتْ لَهُ مَا رَأَتْ فِيهَا مِنَ الصُّوَرِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أُولَئِكَ قَوْمٌ إِذَا مَاتَ فِيهِمُ الْعَبْدُ الصَّالِحُ، أَوِ الرَّجُلُ الصَّالِحُ، بَنَوْا عَلَى قَبْرِهِ مَسْجِدًا، وَصَوَّرُوا فِيهِ تِلْكَ الصُّوَرَ، أُولَئِكَ شِرَارُ الْخَلْقِ عِنْدَ اللهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 434]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -:
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 434]
Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta fadawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta kasance a kasar Habasha ta ga wata coci - ana ce mata Mariya - a cikinta akwai hotuna da kawace- kawace da zane-zane; dan mamaki daga hakan! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana dalilan sanya wadannan hotunan; Sai ya ce: Wadannan wadanda kike fada sun kasance idan mutum nagari ya mutu a cikinsu, sai su gina masallaci akan kabarinsa suna sallah a cikinsa, su kuma zazzana wadancan hotunan, ya bayyana cewa mai aikata wancan shi ne mafi sharrin halitta a wurin Allah - Madaukakin sarki -; domin aikata shi yana kaiwa zuwa shirka da Allah - Madaukakin sarki -.